Ba Zaku Gane Maza Security Ba Ne Ga Mata Sai Mijinki Ya Rasu Ko Kun Rabu -Jamila Ibrahim

Jamila: Duk ranar da akace baki da Aure to fa sai a hankali kin zama hanya mai insecurity, keda hanyar Zamfara ko Rijana na Kaduna kusan daya. Yo harda Wanda Bai isa ya maki magana ba zalyi.
Jamila ta kara da cewa amma in kina daAure koda mijinki baya tabuka maki komal ke kike ciyar dashi mutane ba zasu taba miki kallon banza ba.Don Allah yan uwa mata mune zamu gayawa juna gaskiya idan matsalar da kike fuskanta ba matsala ta transformer ba ce da baya kawo wuta, ba kuma dukanki yake ba kiyiwa Allah kiyi hakuri ki zauna.
Babu Auren da ba’a fuskantar matsala sal dal muce na wani yafi na wani.Babban matsalar bai wuce talauci ba, kuyi hakuri lokaci ne, wannan keburan na taba kowa dan dai mutane basu fito sun fadi matsalarsu ba ne.Ina bawa duk wata matar Aure hakuri, a kara hakuri, Allah ya cigaba da baku hakuri ya biya maku bukatunku na Alkhairi.