Shahararren dan daudun nan da ya mayar da kansa macce ya bayyana cewa yana da juna biyu

Shahararren dan daudunnan na Duniya wanda ya sauya fasalin halittar sa daga Namiji zuwa macce wato Bobrishki ya bayyana cewa yana da juna biyu
Dama a watan disambar daya gabata ne aka ambato shi yana cewa ya fara jinin al’ada kamar yadda mata ke yi sai gashi a halin yanzu yace yana da ciki.
A wani labarin kuma.Gwamnatin tarayya ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a gudanar da babban zaben kasar da ke tafe kamar yadda aka tsara.
Ministan yada labarai Lai Mohammed na ya bayyana haka a Abuja,
a lokacin gabatar da ci-gaban da ma’aikatarsa ta samu karkashin gwamnati mai cl.A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da kalaman da wani babban jami’i a hukumar zaben kasar ya yi na cewa zaben kasar na fuskantar barazanar sokewa saboda matsalar tsaro.
Ministan ya ce matsayar gwamnati ita ce zaben 2023 zal gudana kamar yadda aka tsara.Ya kara da cewa “babu abin da ya faru da yasauya wannan matsayi. Mun sani cewa INEC na aiki da jami’an tsaro domin tabbatar da samun nasarar gudanar da zaben a fadin kasar”.”Hukumomin tsaro na ci gaba da aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa an gudanar da zabukan cikin kwanciyar hankali. Dan haka babu wata fargaba”, in ji ministanHukumar Zabe dai ta saka ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya.