Kannywood
Har Kebe Matata Na Yi A Wuri Daban Saboda Rashin Jituwa Da Yan’uwana
Har Kebe Matata Na Yi A Wuri Daban Saboda Rashin Jituwa Da Yan'uwana

Fitaccen jarumin Kannywood, Adam Zango ya wallafa bidiyoyi yana bayyana yadda suke cikin tsaka mai wuya shi da matarsa.
A cewarsa, ya fito ya yi bayani ne kada a cigaba da kallonsa a matsayin auri-saki. don haka zai wanke kansa daga zargin jama’a.
Ya ce tun farkon aurensu da matarsa ya ce mata ba ya son harkar soshiyal midiya, kuma ta fara bi yanzu ta sauya.
A cewarsa ta wallafa wani bidiyo tana kwasar rawa tare da lalle a jikinta wanda hakan ya sa ya ce ta tafi gidan iyayenta.
Bayan tafiyarta ya bukaci a amshi wayarta don ba ya son rike wayar da ake sanya data don gudun abinda zal je ya dawo.