Kannywood

Bayan Mutuwar Aurena Naga Chanji Dayawa Lokacin Dana Dawo Kannywood Cewar Jaruma Jamila Lasco

Bayan Mutuwar Aurena Naga Chanji Dayawa Lokacin Dana Dawo Kannywood Cewar Jaruma Jamila Lasco

Jarumar Wanda Tayi Sharafinta A duniyar Fina-finan Hausa A Shekarun Baya Sannan Tana Zaune A Garin Kaduna Ta Dawo Masana’antar Kannywood Bayan Mutuwar Aurenta, Amma Sai Dai A Wata hira Da Akayi Da Ita Ta Bayyana irin Chanjin Da Taga A Masana’antar Kannywood.

Sannan Ta Bayyana Yadda Rayuwarta Ta Kasance Acan Baya Da Kuma Yanzu,Duk Dai Acikin Hirar Da Akayi Da Ita Ta Bayyana Haka.

Ki Fadawa Mautane Tarihin Rayuwarki!

Jamila Lasco Tace Ni Dai ‘yar Asalin Kabilar Fulani Ce Ta Janhuriyar Kamaru, Amma Anan Kasar Nigeria Muke zaune Da Iyayena Gaba Daya.

Kina Jin Fulatanchi?

Jamila Tace Inaji Kadan-kadan, Amma Wani Idan Anyi Min Sai Dai Na Maida Da Hausa.

A Wanne Lokaci Kika Shigo Harkar Fina-finan Hausa?

Jamila Lasco Tace Gaskiya Na Dan Taba Harkar A Shekarun Baya, Sannan nayi Aure Daga Nan Kuma Wanda Na Aura Baya Son Na Fara Harkar, kuma Fina-finan Damayi Basu Fita Kasuwa Ba, Ma’ana Ba’a Sansu Ba Sosai.

A Wacce Shekara Kika Fara Harkar?Jamila Lasco Tace Gaskiya Shekaru Da Dama! ta Karasa Maganar Da Dariya.

Zaki Iya Fada Mana Yawan Shekarun?Jamila Tace Zai Iya Kaiwa Shekara 17,Domin Tun Lokacin Su Safiya Musa.Ta Wacce Hanya Kikabi Kika Shiga Harkar Film Din?Jamila Lasco Tace Lokacin Dana Shiga Gaskiya Bansha Wahala Ba,Don Ni Bansha Walaha Ba Kuma Wadanda Suka Sakani A Harkar Sun San iyayena Da ‘Yan Uwana Gaskiya Ban Sha Wahala Ba.Zaki Iya Fitowa Acikin Film Din Da Kika Fito Aciki?Jamila Lasco Tace Gaskiya Film Din Dana Fara Fitowa Bai Fita Kasuwa Ba, Kuma Kasan Shekarun Dayawa, Sai Dai Wadanda Nayi Daga Bayan Nan.A Wancan Lokacin Kina Da Ubangida?Jamila Lasco Tace Bani Da Ubangida.Bayan fitowar ki daga gidan miji, ba ki tunanin sake yin wani auren sai ki ka dawo industiri? Sannan wane kalubale ki ka samu a gidan ku?Shi dai aure lokaci ne. Ko a wancan lokacin ban sa zuwan sa ba, haka yanzu ma idan ya zo ko yau ko gobe a shirye na ke. A gida kuma na fuskanci ƙalubale sosai a wurin mahaifiya ta, don ba ta yarda ba. Sai daga baya, da ɗan bada baki da dai ɗan abubuwa. Ita sai ta gindaya min wasu sharuɗɗa, na yarda, sannan sai ta amince.Bayan Dawowarki Kannywood A Yanzu, Wanne Film Kika Fara?Jamila Tace Bayan na dawo, na fara yi ne da ‘Farin Wata Sha Kallo’ na Adam A. Zango.Zuwa yanzu kin fito a finafinai za su kai nawa?Gaskiya na fito a finafinai za su kai biyar ko ma fiye da haka. Wasu har yanzu ba su fito ba, su na kan hanya. Ka san yadda masana’antar ta ke, wasu finafinan fitowa ɗaya kawai za ka yi, wasu fitowa biyu, akwai ire-iren su da dama. Wasu kuma ban ma san sunan su ba.Da ki ka dawo industiri, ya ki ka ga yanayin masana’antar a da da kuma yanzu?Jamila Tace Gaskiya akwai bambanci sosai, domin yadda ake tafiyar da al’amuran masana’antar a da da kuma yanzu ba ɗaya ba ne. A da kafin a saka ka a fim sai an duba bajintar ka da kuma yanayin yadda ka ke gudanar da aktin ɗin ka. Amma ba kamar yanzu ba da sai ka na da uwa a gindin murhu, ma’ana da ƙwauri sai gwiwa; wani in ba ka na da wata alaƙa da shi ba ba zai saka a fim ɗin sa ba, kuma ko fim nawa zai yi. Sai kawai idan Allah ya sa ka na da rabo sai ka ga an saka ka ko da kuwa ba wani mutunci ku ke yi ba.Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Tarihi Na Wannan Jarumar, Sannna Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.Ku Karanta Wannan Labarin:

Share to

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button