
A wata fira da aka yi tare da safara’u kwana casa’in ta bayyana irin mawuyacin halin da ta shiga lokacin da taji labarin bidiyon ta ya yadu a duniya a ko wata kafar sada zumunta maganar da ake kenan.
Ta bayyana “ta shiga halin da sai da tafi son mutuwa akan rayuwa sannan ta bayyana ta kusan wata ukku a gida bata fita waje saboda tana fita za’a fara jifar ta da duwatsu ana fadi mata maganganu mara su dadi.
Sannan ta bayyana cewa “ita tayi wannan bidiyo ne dan nishadi ba wai dan ta turawa wani ba kuma tasan cewa daya daga cikin kawayen tane suka fidda wannan bidiyo a kafafen sada zumunta.”
Safara’u ta kara da cewa “ba ita kadai ba mafiyawancin mata yan uwan ta suna da irin wadannan bidiyoyin a wayoyin su shawara shine su san wadanda zasu dinga bai wa wayar su.”
Wannan itace babbar fira da akayi da jarumar wacce yanzu ta koma mawakiyar hip hop. Ga bidiyon nan mun kawo maku ga masu sha’awar gane wa idon su. Gidan jaridar BBC Hausa ne suka gudanar da wannan fira.