
Jami’an hukumar Hisbah a Kano sun daƙumo matashin mawaƙin nan Al’ameen G-Fresh.
An kuma gurfanar da shi a hukumar bisa zargin wasa da Sallah a wani faifan bidiyo da wasu suka ɗauke shi, sannan suka yaɗa a dandalin TikTok.
Jami’an na Hisbah sun yi masa nasiha tare da bashi shawarar ya koma Makaranta, nan take kuma ya miƙa wuya.
Ku kalli yadda ta kasance da shi a hukumar ta Hisbah.