Labarai
Innalilahi Wainaa ilaihirajiun Yan Ta’adda Sun Shiga Har Gida Sun Yi Masa Yankan Rago, Allah Ya Gafarta Masa
Innalilahi Wainaa ilaihirajiun Yan Ta’adda Sun Shiga Har Gida Sun Yi Masa Yankan Rago, Allah Ya Gafarta Masa

A jiya da daddare ne Allah ya yi wa Mansur Kasuwar Mata Karamar hukumar Dandume dake jihar Katsina rasuwa, sanadiyyar ‘yan ta’adda da suka shiga har gidan sa suka yi masa ýanķàñ ŕago, bayan haka suka faŕķè cikin sa, suka ýàñka bakinsa biyu, tare da yi masa munanan sara a jikinsa.
Za a yi jana’izar sa da misalin karfe 10 na safe, a gidan Alhaji Ummaru Mai ‘Yan Kudi, kusa da Plaza ta Hamisu Manaja Dandume.
Ya Allah muna rokon ka da sunayen ka tsarkaka Allah ka bi masa hakkinsa, ya kuma tona asirin wadanda suka yi mashi wannan aika-aikar. Allah ka jikansa da rahmarka, ya kuma kare mu da karewar sa.